Gwamnatin tarayya ta bayyana damuwarta kan yadda matsalolin sauyin yanayi ke cigaba da barazana ga tattalin arzikin kasa

0 71

Gwamnatin tarayya ta bayyana damuwarta kan yadda matsalolin sauyin yanayi ke cigaba da barazana ga tattalin arzikin kasa.

Babbar sakatare mai kula ayyukan ofishin muhalli Habiba Lawan ta bayyana haka a abuja, a yayin ziyarar ban girma da mahalarta taron Cibiyar Nazarin Tsaro ta kasa suka kai ofishinta a Abuja, ta ce karuwar yawan al’umma ya haifar da rashin tsaro da rikice-rikice, wanda ke kawo cikas ga zaman lafiya a Afirka sakamakon matsin lamba kan albarkatun.

Ta bukaci hukumar ta bullo da aiwatar da manufofin da za su magance rikice-rikice masu alaka da sauyin yanayi a kan iyakokin Afirka.

Ta ce rahoton tantancewa karo na 5 na kwamitin gwamnatoci kan sauyin yanayi, ya nuna karara cewa duniya na samun dumamar yanayi fiye da yadda aka yi kiyasin a baya, kuma mutane ne ke haifar da mafi yawan irin wannan sauyi.

Illar sauyin yanayi, na shafar harkokin noma, zaman lafiya, makamashi, lafiyar dan Adam, yanayin kasa da na ruwa da dai sauransu, musamman a nahiyar Afirka.

Leave a Reply

%d bloggers like this: