

- Yadda yan IPOB suka kashe ‘yan Arewa 10 ciki har da mace mai juna biyu da ‘ya’yanta 4 da wasu mutane 6 a jihar Anambra - May 24, 2022
- Sama da mutane 30 ne aka ruwaito sun bace a jihar Borno bayan da wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne suka kai musu hari - May 24, 2022
- Tsohon gwamnan jihar Gombe, Ibrahim Dankwambo, ya karbi tikitin takarar Sanatan Gombe ta Arewa domin tsayawa takara a jam’iyyar PDP a 2023 - May 24, 2022
Gwamnatin tarayya a jiya ta ce kimanin rigakafin Cutar Corona Miliyan 3 da dubu 500 ta Prizer take tsammanin zuwan ta daga kasar Amurka, domin cigaba da yiwa yan kasar rigakafin cutar.
Da yake yiwa manema labarai Jawabi, Shugaban Kwamatin Yaki da Cutar na Kasa Boss Mustapha Gida, ya ce an samu cigaba a rigakafin cutar.
A cewarsa, kimanin allurar rigakafin Miliyan 3 da dubu 500 suke tsammani daga kasar Amurka cikin watan nan, inda ya kara da cewa suna tsammanin wata rigakafin kimanin Miliyan 4 ta AstraZeneca a wata mai zuwa.
Boss Mustapha, ya ce kwamatin sa yana sane da irin yanayin wahalhalun da Matafiya suke ciki, musamman wadanda suke duba shafukan Internet na Matafiya.
Boss Mustapha ya koka kan yadda wasu Ma’aikatan filayen jirgi suke kin gudanar da ayyukansu cikin tsari ta hanyar killace matafiyan.
Shugaban Kwamatin wanda kuma shine Sakataren Gwamnatin tarayya ya ce hukumomin suna cigaba da bincike kan zarge-zargen da ake yiwa wasu ma’aikatan filayen jarage.