Gwamnatin tarayya ta ce ta samar da ayyukan yi sama da dubu 74 ga yan Najeriya ta hanyar aiwatar da shirin ayyukan muhalli

0 71

Gwamnatin tarayya ta ce ta samar da ayyukan yi dubu 74,413 ga yan Najeriya ta hanyar aiwatar da shirin ayyukan Muhalla a kasar nan.

Karamar Ministar Muhalli ta Kasa Chief Sharon Ikeazor, ita ce ta bayyana hakan a lokacin taron Majalisar Muhalli karo na 15 wanda aka gudanar jiya a Abuja.

Misis Sharon ta ce ayyukan sun samu ne ta hanyar yin hadin gwiwa da tsakanin Ma’aikatar da kuma sauran Kamfanoni masu zaman kansu a kasar nan.

Ministar ta ce Ma’aikatar tana aiki tukuru domin ganin cewa ta cimma yarjejeniyar data sanyawa hannu a birnin Paris, inda ta kara da cewa gwamnatin tana aiki sosai domin ganin cewa ta cimma nasara.

Kazalika, ta ce wasu daga cikin Nasarorin da aka cimma sun hada da Daftarin Sauyin Yanayi na Kasa, wanda Majalisar Zartarwa ta Kasa ta amince da dashi a watan Yuni.

Leave a Reply

%d bloggers like this: