Gwamnatin tarayya ta ce zata sake karbo wasu kudade mallakin Najeriya wanda aka boyesu a kasar Amurka

0 67

Gwamnatin tarayya ta ce zata sake karbo wasu kudade mallakin Najeriya wanda aka boyesu a kasar Amurka wanda yawan su yakai kimanin Fan Miliyan 200.

Babban Lauyan Gwamnati kuma Ministan Shari’a na Kasa Abubakar Malami SAN, shine ya bayyana hakan a birnin New York na kasar a taron Majalisar Dinkin Duniya.

Da yake magana kan yaki da cin hanci da rashawa, Ministan ya ce gwamnatin tarayya tana kokarin dawo da Kudaden da suka kai Fan Miliyan 200 zuwa kasar nan, sai dai ya ce wannan ba yana nufin cewa babu kadarori da za’a sake kwatowa ba.

Ministan ya ce, ba ya so ya bayyana hanyoyin da gwamnatin tarayya take bi wajen kwato kadarorin.

Haka kuma ya ce gwamnatin tarayya tana bin hanyoyin da suka kamata wajen dawo da kudaden da kadarorin ta hanya mai sauki.

Kazalika, ya ce gwamnatin tarayya ta jajirce wajen yaki da cin hanci da rashawa, ta hanyar karbo kudaden da aka sace.

Leave a Reply

%d bloggers like this: