Gwamnatin tarayya ta dawo da wasu Yan Najeriya 166 da suka makale daga kasar Libya a wani yunkuri da sukeyi domin tsallakawa nahiyyar Turai ci rani

0 87

Gwamnatin tarayya ta dawo da wasu Yan Najeriya 166 da suka makale daga kasar Libya a wani yunkuri da sukeyi domin tsallakawa nahiyyar turai ci rani.

Shugaban Ofishin Jakadancin Najeriya a Libiya Kabiru Musa ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya rabawa manema labarai jiya a Abuja.

Musa ya ce mutane 166 da aka kwaso, sun tashi daga filin jirgin saman Mitiga na birnin Tripoli kuma ana sa ran isarsu Najeriya ta filin jirgin sama na Murtala Muhammed da ke Legas.

Ya ce gwamnatin tarayya tare da hadin gwiwar hukumar kula da Yan cirani ta kasa da kasa ne suka gudanar da aikin kwashen mutanen da kuma goyon bayan hukumomin kasar Libya.

Ya kuma kara da cewa, kamar yadda aka saba, an shirya tarbar mutanen daga zarar sun iso Najeriya.

Za’a kuma a hada su da iyalansu daga zarar an kammala shirye shirye.

Leave a Reply

%d bloggers like this: