Shugaba Buhari ya ce nahiyar Afirka na bukatar samar da makamashin wuta mai dimbin yawa domin bunkasar ta saboda sauyin yanayi

0 76

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce nahiyar Afirka na bukatar samar da makamashi mai dimbin yawa domin bunkasar ta, duba da yadda duniya ke yaki da sauyin yanayi.

Buhari wanda Ministan ma’adinai da karafa Olamilekan Adegbite ya wakilta, a wajen wani taron kwanaki uku na zuba jari na Najeriya da Afirka wanda aka gudanar a babban Abuja.

A  taron wanda aka masa lakabi da koren Afirka.

Buhari yace, ana bukatar Afirka ta samu karfin samar da makamashi mai yawa, domin duniya na kau da kai daga man fetur zuwa ga tsaftataccen makamashi mai tsafta.

Ya ce wannan sauyin makamashin na tattare da kalubale da damammaki ga nahiyar dake muradin samun ci gaba.

Ya yi imanin cewa hakan, maida Afirka zuwa nahiyar da ke da mutane daban-daban, tare da hadin gwiwa wajan bullo da sabbin hanyoyin warware matsaloli.

Leave a Reply

%d bloggers like this: