Hukumar dakile bazuwar Cututtuka ta kasa (NCDC) ta ce akalla mutane 54 ne suka mutu sakamakon kamuwa da cutar kwalara a Najeriya

0 88

Hukumar dakile bazuwar Cututtuka ta kasa (NCDC) ta ce akalla mutane 54 ne suka mutu sakamakon kamuwa da cutar kwalara a kasarnan.

A cikin sabon rahotonta, NCDC ta bayyana cewa an samu rahoton mutuwar mutanen ne tsakanin 1 ga watan Janairu zuwa 1 ga Mayu, 2022.

Ta kara da cewa, an kuma samu sama da mutane 1,800 da ake zargin sun kamu da cutar a kananan hukumomi 77 dake fadin jihohi 16 na kasarnan.

Jihohin sun hada da Abia, Adamawa, Akwa Ibom, Bauchi, Bayelsa, Borno, Cross River, Katsina, Kebbi, Kwara, Lagos, Nasarawa, Ondo, Rivers, Taraba, da Zamfara.

Ya zuwa ranar 1 ga Mayu, 2022, adadin mutane 1,861 da ake zargin sun kamu da wannan cutar, ciki har da mutuwar 54 daga jihohi 16 a bana.

A cewar hukumar, kananan hukumomi 12 suna samun rahoton bullar cutar fiye da 30 a kowacce shekara.

Leave a Reply

%d bloggers like this: