Najeriya ta tafka asarar fiye da Naira biliyan 430 na satar danyen mai a cikin wata uku

0 82

Shugaban hukumar da ke sa ido kan kan man da ake hakowa a kan tudu, Mista Gbenga Komolafe, ya ce Najeriya ta tafka asarar kusan naira biliyan 434 saboda satar da ake yi na mai tsakanin watan Janairu zuwa Maris din wannan shekarar.

An tafka wannan asara ce adaidai lokacin da karaminin Ministan man fetur, Mista Timipre Sylva, ke cewa kamfanonin mai masu zaman kansu a Najeriya na barin kasar saboda hadarin da suke fuskanta.

Shi ma, attajirin Afirkan nan kuma shugaban rukunni kamfanin Dangote, Alhaji Aliko Dangote ya shawarci gwamnatin Najeriya ta fito da tsarin bai-daya kan kudaden haraji domin karfafawa masu zuba jari a fanin hako mai ta tudu da kuma cikin teku.

Komolafe ya ce an iya fitar da gangan miliyan 1.35 ko kashi 71 cikin 100 na gangan miliyan 1.9 da ake samarwa, saboda satar da ake fuskanta da farfasa batutan mai.

Ya kuma jadada cewa wannan na daga cikin matsalolin da ke sake kassara Najeriya.

Leave a Reply

%d bloggers like this: