Gwamnatin tarayya ta kafe kan cewa ba a harbi masu zanga-zanga a Lagos ba, a rana mai kamar ta yau a bara.

Jami’an tsaro sun yi amfani da karfin tuwo wajen tarwatsa masu zanga-zangar EndSARS, wadanda ke zanga-zanga akan cin zarafin da yansanda ke yi, shekara guda kenan daidai.

Bayan wadanda suka shirya zanga-zangar sun dage kan cewa an kashe wasu masu zanga-zangar, gwamnatin tarayya tayi watsi da rahoton kashe-kashen.

A wajen taron manema labarai yau a Abuja, ministan labarai, Lai Mohammed, yace shekara guda bayan lamarin, har yanzu babu shaidar an kashe mutane.

A wani labarin kuma, wasu masu zanga-zangar EndSARS a yau sun bazama kan tituna a Abuja domin tunawa da cika shekara guda da zanga-zangar.

Masu zanga-zangar sun hallara a dandalin Unity dake Abuja, kafin su bazama kan tituna.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: