Za a gudanar da jarabawar komputa ga matasan da suka nemi shiga aikin dansanda

0 140

Rundunar ‘yansanda ta kasa tare da hadin gwiwar hukumar lura da al’amurran yansanda ta kasa da kuma hukumar shirya jarabawa ta WAEC zasu gudanar da jarabawar komputa ga matasan da suka nemi shiga aikin dansanda.

A sanarwar da kakakin rundunar yansanda ta jiha ASP Lawan Shiisu Adam ya fitar, tace matasan da zasu rubuta jabarawar sune wadanda aka tantance a kwanakin baya a helkwatar yansanda ta jiha dake Dutse.

Sanarwar ta kara da cewar za a gudanar da jarabawar ne a ranakun 29 zuwa 30 ga watan da muke ciki, kuma za a sanar da wajen gudanar da jarabawar a nan gaba.

Dan haka sanarwar ta bukaci matasan da su duba sunayensu a shafin daukar aikin dansanda na hukumar ta internet.

Leave a Reply

%d bloggers like this: