Wasu bama-bamai a gefen hanya guda biyu sun tashi a kusa da wata mota kirar bus dake dauke da sojoji a Damashka, babban birnin kasar Sham, inda suka kashe jami’an sojoji 13 tare da raunata wasu 3.

Harin wanda ya auku a safiyar yau shine mafi muni a Damashka cikin shekaru, kuma wanda ba a saba gani ba tun bayan da dakarun soji suka kwace iko da kauyukan da a baya suke karkashin mulkin dakarun ‘yan adawa a rikicin kasar Sham na shekara 10.

Gidan talabijin na gwamnatin kasar ya nuna faifan bidiyon motar kirar bus a tsakiyar Damashka, inda yace harin ya auku a lokacin da mutane ke fitowa daga gidajensu zuwa makarantu ko wajen aiki.

Gidan talabijin din yace bama-baman 2 sun tarwatse a lokacin da motar take kusa da gadar Hafez al-Assad, inda ya kara da cewa sojojin sun samu nasarar lalata bam na uku, a lamarin da jami’ai suka kira da harin ta’addanci.

Kawo yanzu babu wanda ya dauki alhakin kai harin.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: