‘Yansanda a jihar Imo sun tabbatar da kisan wasu sarakunan gargajiya guda biyu a jihar

0 84

‘Yansanda a jihar Imo sun tabbatar da kisan wasu sarakunan gargajiya guda biyu a jihar.

Kakakin ‘yansanda na jihar ta Imo, Mike Abattam, yace lamarin ya faru ne a jiya a garin Nnenasa dake karamar hukumar Njaba ta jihar.

Mike Abattam yace ‘yansanda na binciken kashe-kashen domin tabbatar da lamarin da ya haifar da aukuwar hakan.

An ce wasu ‘yan bindiga sun mamaye wajen wani taro inda sarakunan gargajiya da masu ruwa da tsaki suka hallara a garin Nnesa a jiya, kuma suka bude musu wuta inda suka kashe sarakuna biyu nan take.

Harbe-harben ya jawo mahalarta taron sun gudu domin tsira da rayukansu.

Mutane dayawa a wajen taron sun samu raunuka kuma babu wata kungiya da ta dauki alhakin kai harin.

Leave a Reply

%d bloggers like this: