Gwamnatin Tarayya ta raba Naira biliyan 1 da Miliyan 300 ga masu karamin karfi dubu 100 ta cikin shirin yaki da fatara a jihar Katsina

0 47

Gwamnatin tarayya ta raba kimanin Naira Biliyan 1 da Miliyan 300 da masu karamin karfi dubu 100 da 043 ta cikin shirin yaki da Fatara a Jihar Katsina.

Shirin Yaki Da Fatara ga Masu Karamin Karfi, shiri ne da Gwamnatin tarayya ta kirkira domin tallafawa masu karamin karfi, a wani mataki da dakile talauci tare da bunkasa tattalin arzikin ga Al’umma.

Mai Mataimakawa Jihar Gwamnan Katsina kan Sana’oin Dogaro da Kai da kuma Shirye-Shiryen Tallafi Hon Abdulkadir Mamman-Nasir, shine ya bayyana hakan a lokacin da masu cin gajiyar shirin suka shirya wani gangamin a Katsina.

Hon Mamman-Nasir wanda kuma shine shugaban Ofishin Shirin yaki da talauci na kasa reshen Jihar Katsina, ya bayyana cewa kowanne mutum daya ya samu Naira dubu 10,000 cikin watanni 2 da suka gabata.

Haka kuma ya ce Gwamnatin tarayya ta kashe Naira Biliyan 1 da Miliyan 100 domin bada abinci kyauta ga Dalibai dubu 800,000 wanda suke Makarantun Firamare dubu 2,777 a Jihar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: