Gwamnatin tarayya ta sauya wa wasu filayen jiragen sama suna

0 256

Gwamnatin tarayya karkashin jagorancin shugaba Bola Tinubu ta sauya wa wasu filayen jiragen sama na tarayya sunayen wasu fitattun ‘yan Najeriya.

Hakan ya fito ne a wata takarda da ma’aikatar sufurin jiragen sama ta tarayya mai dauke da sa hannun Misis Joke Olatunji daraktan ayyuka na filin jirgin.

Sanarwar da aka rabawa manema labarai ta ce shugaban ya sauya wa filayen jiragen saman suna a matsayin wani bangare na garambawul a bangaren sufurin jiragen sama.

An canza sunan filin jirgin saman Maiduguri da sunan tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari da filin jirgin sama na Fatakwal da sunan marigayi dan kishin kasa Obafemi Awolowo, yayin da filin jirgin saman Nasarawa ya koma sunan marigayi Usman Dan Fodio wanda ya kafa Daular Sokoto. Har ila yau, an sauya sunan filin jirgin saman Benin da sunan marigayi Oba na Benin, Oba Akenzua II, filin jirgin sama na Ebonyi da sunan tsohon shugaban majalisar dattawa, Chuba Okadigbo, da filin jirgin saman Ibadan da sunan tsohon Firimiyan Yamma Ladoke Akintola.

Leave a Reply

%d bloggers like this: