

- Wasu ‘yan bindiga sun kashe wakilai uku na ‘yan takarar gwamna na jam’iyyar PDP daga karamar hukumar Mariga ta jihar Neja - May 26, 2022
- Dalilan da yasa wasu ‘yan takarar gwamna 2 na jam’iyyar APC suka yi watsi da zaman ganawar da gwamna Badaru ya kira domin a samar da dan takarar daya tal - May 26, 2022
- Mataimakin kwamishinan ‘yan sandan da aka dakatar, Abba Kyari ya garzaya wata babbar kotun tarayya domin neman belinsa - May 26, 2022
Gwamnatin Tarayya tace ta fito da wasu lambobi na komfuta domin maye gurbin takardar shaidar zama dan kasa.
Ministan sadarwa da tattalin arzikin komfuta, Isa Ali Pantami, ya fadi haka a wani taron karawa juna sani akan canja lambar shaidar zama dan kasa, wanda hukumar shaidar zama dan kasa ta shirya a Abuja.
Yace gwamnati ta amince da fasahar domin tabbatar da tsaron sirrikan mutane da bayanansu, da kuma rage yawaitar samun lambar zama dan kasa ba bisa ka’ida ba.
Ministan wanda ya samu wakilcin darakta janar na hukumar shaidar zama dan kasa, Aliyu Abubakar, yace za a fara amfani da sabbin lambobin daga ranar 1 ga watan Janairun da za mu shiga.
Aliyu Abubakar yace manufar shirin shine tattaunawa kafada da kafada da masu ruwa da tsaki domin tabbatar da fahimtar lambar.