

- Mataimakin Gwamnan jihar Jigawa, Mallam Umar Namadi, shine ya lashe zaben fidda gwani na dan takarar gwamna a jam’iyyar APC - May 27, 2022
- Shugaba Buhari yace gwamnatinsa tana assasa ginshiki mai inganci na kyakykyawar rayuwa domin yara manyan gobe a Najeriya - May 27, 2022
- Rundunar ‘yan sandan jihar Jigawa ta haramta bangar siyasa da tare da yin amfani da duk wani makami ga yaran yan siyasa - May 27, 2022
Al’umomin jihar Barno a Najeriya sun ce kawo yanzu babu labarin dalibai mata 110 daga cikin 276 da mayakan boko haram suka sace a Sakandaren Chibok tun shekarar 2014.
Wata kungiyar raya Yankin Chibok din, wadda ke sahun gaba wajen ganin an ceto Yam matan ta hannun shugaban ta Dauda Iliya tace daga cikin daliban 276, 57 sun yi nasarar gudu daga hannun wadanda akayi garkuwa da su
shugaban kungiyar yace daga shekarar 2012 zuwa yanzu an kashe mutane sama da 72 a yankin, yayin da aka sace sama da 407, tare da kona gidaje da wuraren sana’oi da mujami’u da kayan abinci da kuma sace motoci sama da 20.
ya kara da cewa, daga karshen shekarar 2018 zuwa yanzu, mayakan book haram sun kai hare haren a yankin, ciki harda wanda aka kai kautikari a ranar 14 ga wannan wata inda aka sace Yam mata 5 tare da kashe mutane 3 da kuma kona gidaje da mujami’u.
Jami’in yace har yanzu suna jiran hukumomin Najeriya su ceto musu dalibai mata 110 da aka sace a shekarar 2014, tare da bukatar kara yawan sojoji da kayan aiki a Chibok domin dakile hare haren da ake kai musu.