’Yan Bindiga Sun kashe Mutane Da Dama da Kone Gidaje A Neja

0 81

’yan bindiga suka hallaka mutane da dama tare da kone gidaje masu yawa a wani sabon hari da suka kai yankunan Galadima-Kogo da Galkogo a Karamar Hukumar Shiroro ta Jihar Neja.

Rahotanni sun bayyana cewa yan bindigar sun kai harin ne dauke da muggan makamai inda suka afkawa kauyukan bayan sunci karfin jami’an tsaro.

kazalika, mazauna yankunan da ke da makwabtaka da kauyukan da maharan suka afka, irin su Kuchi da Sabon kabula da Kafana da Dangunu da Zazzaga da kuma Chibani na Karamar Hukumar Munya,suna guduwa na barin matsugunnan su.

Kakakin Rundunar ’Yan Sanda ta Jihar Neja, DSP Wasiu Abiodun,bai ce komai ba kan wannan batu.

Sai dai Kwamishinan Kananan Hukumomi, Al’amuran Cikin Gida na Jihar Nejan Emmanuel Umar, ya tabbatar faruwar lamarin ga manema labarai.

“An farmaki guda daga cikin sansanonin jami’an tsaronmu da ke yankin yayin harin. Amma muna nan muna shirye-shiryen fatattakar yan bindigar, inji Kwamishinan Kananan Hukumomi na Jahar Nejan.

“Yanzu haka, akwai aikin hare-haren da ake kai musu ta sama da ta kasa, muna iya bakin kokarinmu,” kamar yadda Kwamishinan yace.

Shi ma Shugaban Karamar Hukumar Shiroro, Sulaiman Dauda Chukuba, ya tabbatar faruwar kai harin.

Leave a Reply

%d bloggers like this: