Hukumar DSS tana zargin Mallam Tukur Mamu a matsayin wanda yake taimakawa yan ta’adda da bayanan sirri

0 63

Hukumar Tsaro ta Farin Kaya wato DSS ta zargi Mallam Tukur Mamu, mai shiga tsakin yan bindiga da kuma mutanen da aka sace, a matsayin mutumin da ya ke taimakawa yan Ta’adda da Ta’addanci.

Hukumar DSS ta yi zargin cewa Mamallakin Jaridar ta Desert Herald, ya na da hannu a tallafawa yan Ta’adda da kudade na Ciki da Wajen Kasar nan.

Haka kuma ta zargi Mallam Tukur Mamu da fadawa yan ta’addar bayanin sirri na tsaro wanda hakan ne ya haifar da yawan karuwar hare-hare a kasar nan.

Kamfanin Dillancin Labarai na Kasa NAN, ya rawaito cewa a jiya ne Alkalin Kotun da aka gabatar da Tukur Mamu, ya amincewa Hukumar DSS ta cigaba da tsare shi har tsawon Kwanaki 60 domin kammala bincike, bayan Lauyan DSS Barista Ahmed Magaji, ya gabatar da bukatar hakan.

Manema Labarai sun rawaito cewa Hukumar DSS ce ta kama Mallam Mamu a filin Jirgin Saman Kasa-Da-Kasa na Mallam Aminu Kano, bayan an dawo dashi daga Kasar Egypt a lokacin da yake kokarin tsallakawa zuwa Saudi Arabia domin yin aikin Hajji.

Mallam Tukur Mamu de, shine Mai mutumin da yake shiga Tsakani domin kubutar da mutanen da yan bindiga suka yi garkuwa da su a hanyar Jirgin kasan Kaduna zuwa Abuja cikin watan Maris na wannan shekara.

Leave a Reply

%d bloggers like this: