Hukumar kashe gobara ta kasa tace gobarar da aka samu a ginin ma’aikatar kudi yau da safe karama ce wacce ta shafi batira kadai
Hukumar kashe gobara ta kasa tace gobarar da aka samu a ginin ma’aikatar kudi yau da safe karama ce wacce ta shafi batira kuma an gaggauta dakile ta.
Kakakin hukumar, Abraham Paul, ya gayawa manema labarai cewa lamarin ya faru ne a kasan ginin ma’aikatar inda aka ajiye batiran.
Yace babu wanda ya rasu kuma babu wanda ya samu wani baban rauni. Amma akalla manyan batira 20 sun lalace.
A nasa jawabin, kakakin ma’aikatar ta kudi, Olajide Osundun, yace wutar ta tashi da misalin karfe 6 da mintuna 50 na safe lokacin da wasu ma’aikatan ma’aikatar suka ga hayaki na fitowa daga wajen.
Kakakin yace an shawo kan wutar bayan mutane sun kawo dauki.
Gobarar a ma’aikatar na zuwa ne kimanin makonni 2 bayan an samu wata babbar gobara a wata hukumar ta gwamnati.