Mutane biyu sun mutu kuma wasu uku sun jikkata a wani mummunan hadarin mota a kauyen Munkawo dake yankin karamar hukumar Birniwa ta jihar Jigawa.

Kakakin hukumar tsaron fararen hula civil defense a jiharnan, Adamu Shehu, ya tabbatar da hakan ga manema labarai.

Yace hadarin ya auku a jiya da rana akan Birniwa zuwa Mallam-Madori.

Adamu Shehu ya bayyana cewa hadarin ya auku lokacin da sitiyari ya kwacewa direban wata mota kirar Sharon kuma ya take wani babur.

Yace hatsarin ya rutsa da mutane 5, biyu daga cikinsu sun mutu yayin da sauran ukun suka samu raunuka.

Kakakin hukumar yace an aika da wadanda suka jikkata zuwa babban asibitin Birniwa domin a duba lafiyarsu yayin da aka ajiye gawarwakin a wajen ajiyar gawarwaki na asibitin.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: