Labarai

Hukumar kula da tashoshin jiragen ruwa ta Najeriya ta ce ana sa ran jiragen ruwa 13 a tashar ruwan Legas cike da kayan abinci da man fetur

Hukumar kula da tashoshin jiragen ruwa ta Najeriya a jiya ta ce ana sa ran jiragen ruwa 13 a tashar ruwan Legas daga ranar 6 ga watan Yuni zuwa 14 ga watan Yuni.

Hukumar ta ce jiragen na dauke ne da kayayyakin man fetur, da kayan masarufi, da daskararren kifi, da kwantenoni, da sukari mai yawa, da iskar gas da sinadarin gypsum mai yawa da alkama.

Hukumar ta bada rahoton cewa wasu jiragen ruwa guda uku ne suka isa tashar jiragen ruwa kuma suna jiran a sauke musu kaya.

Har ila yau, hukumar ta ce wasu jiragen ruwa 19 ne a tashar jiragen ruwa da ke dauke da alkama, kayan masarufi da daskararren kifi, da kwantenoni, da sukari mai yawa, da sinadarin gypsum mai yawa, da man fetur na mota da kuma man gas.

A wani labarin kuma, Hukumar hana fasa kwauri ta kasa kwastam, reshen jihar Neja ta ce ta kama wasu manyan motoci guda 101 da yadi da tagulla da kayan masarufi da kudinsu ya kai naira miliyan 755 da dubu 300 a sassa daban-daban na yankin.

A cewar ma’aikatar, kayayyakin da aka kama sun hada da ruwan roba da giya da tumaturin gwangwani da taliya ‘yar kasar waje da shinkafa ‘yar kasar waje, da man girki, da sauran su.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: