Hukumar NCDC ta ce kimanin mutane Miliyan 3 da dubu 487 da 298 ne aka kammala yi musu rigakafin cutar Corona a Najeriya

0 64

Hukumar Lafiya a Matakin Farko ta Kasa ta ce kimanin mutane Miliyan 3 da dubu 487 da 298 ne aka kammala yi musu rigakafin cutar Corona a Najeriya, bayan sun karbi rigakafin cutar a karo na biyu.

Sakataren Zartarwa na Hukumar Lafiya a matakin farko na Kasa Dr Faisal Shu’aib, shine ya bayyana hakan a lokacin da yake kaddamar rigakafin cutar a birnin Lafia na Jihar Nasarawa.

Dr Faisal Shua’ibu, ya bayyana cewa zuwa jiya kimanin mutane Miliyan 6 da dubu 242 da 224 ne aka musu rigakafin cutar a karon farko a kasa baki daya.

Haka kuma ya ce gwamnatin tarayya ta bullo da hanyoyin shirya gangamin rigakafin cutar, domin rage yaduwarta a cikin Al’umma.

A jawabinsa, Gwamnan Jihar Nasarawa Abdullahi Sule, ya bada tabbacin cewa gwamnatinsa, zata tabbatar da cewa duk mazauna Jihar sun sami rigakafin cutar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: