Hukumar NDLEA ta kama akalla mutane 303 da ake zargi da safarar miyagun kwayoyi a jihar Kaduna

0 78

Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi NDLEA reshen jihar Kaduna tace jami’anta sun kama akalla mutane 303 da ake zargi da safarar miyagun kwayoyi a watannin ukun farkon 2022 a jihar Kaduna.

Kwamandan NDLEA na jihar, Umar Adoro, shine ya sanar da haka ga kamfanin dillancin labarai na kasa yau a Kaduna.

Umar Adoro yace mutane 303 da ake zargi da safarar miyagun kwayoyi sun hada da maza 291 da mata 12.

Ya lissafa kwayoyin da aka kwace cikin watannin da suka hada da tabar wiwi da hodar iblis da tramadol da sauransu.

Ya sanar da cewa daga cikin mutanen 303 da ake zargi, ana gyaran tarbiyyar 155, yayin da aka gurfanar da 74 a gaban kotu, inda aka yankewa 26 hukunci, sauran 39 suna cigaba da fuskantar bincike, sai 8 da aka mika su ga hannun sauran hukumomin tsaro.

Leave a Reply

%d bloggers like this: