Hukumar SSS ta ankarar da al’umma akan yiwuwar kai harin ta’addaci a ranar Sallah

0 326

Hukumar tsaro ta farin kaya ta kasa SSS a Abuja, ta gargadi jama’a da su yi taka-tsan-tsan da hare-haren ‘yan ta’adda a yayin bikin Babbbar sallar ta bana.

Mai magana da yawun hukumar, Peter Afunanya ya bayyana cewa rahotannin da suka samu ya nuna cewa akwai shirin kai hari kan wuraren ibada, da wuraren shakatawa, kafin sallah, lokacin sallah da kuma bayan Sallah.

A cewarsa, yanzu haka sun kwato wasu bama-bamai, daga hannun ‘yan ta’addan yayin wani aikin hadin gwiwa da suka yi.

Ya kuma bayyana cewa, sashen ya kai samame a maboyar ‘yan ta’adda a jihohin Kogi da Nasarawa a cikin makon nan tare da hadin gwiwar sojojin Najeriya da rundunar ‘yan sandan Najeriya.

Mista Afunanya ya kara da cewa, samamen da suka kai kan titin Abuja zuwa Keffi a karamar hukumar Keffi ta jihar Nasarawa ya kai ga kama wani da ake zargin dan bindiga ne. Ya kuma umarci ma’aikata da masu kula da wuraren taruwar jama’a da suka hada da kasuwanni da kantuna da su kasance cikin shiri da kuma kai rahoton duk wani motsi da suke da shakku a kai ga hukumomin tsaron da abin ya shafa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: