Hukumar tara kudaden shiga ta tarayya tace tana shirin fito da tsarin karbar harajin amfani da titunan mota a kasarnan

0 61

Hukumar tara kudaden shiga ta tarayya tace tana shirin fito da tsarin karbar harajin amfani da titunan mota a kasarnan, domin kara samun kudaden shiga.

Shugaban hukumar, Muhammad Nami, ya sanar da haka da haka a jiya lokacin da ya karbi bakuncin tawagar kungiyar ‘yan jaridu ta kasa, karkashin jagorancin shugaban kungiyar na kasa, Chris Isiguzo, a ofishinsa dake Abuja.

Mataimaki na musamman kan yada labarai da sadarwa na shugaban hukumar, Johannes Wojuola, ya sanar da haka ga manema labarai cikin wata sanarwar da ya fitar jiya.

An bayar da rahoton cewa Muhammad Nami yace tsarin harajin da ake shirin fitowa da shi, wanda hukumar zata kula da karbarsa, zai samarwa da gwamnati isasshen kudaden gina tituna da gyaransu, da kuma samar da tsaron da ake bukata a kasarnan.

Da yake cigaba da jawabi, Muhammad Nami, ya bayyana cewa tattalin arzikin kasarnan a halin yanzu ya dogara ne kacokan kan kudaden shigar da ba na man fetur ba, wajen biyan albashi da samar da ababen more rayuwa ga jama’a.

Leave a Reply

%d bloggers like this: