Shugaba Buhari ya umarci sojoji da sauran hukumomin tsaro da su tabbatar anyi zaben gwamnan Jihar Anambra

0 71

Shugaban kasa Muhammad Buhari ya umarci sojoji da sauran hukumomin tsaro su tabbatar cewar babu abin da ya hana zaben gwamnan da za ayi a Jihar Anambra a ranar 6 ga watan Nuwamba.

Mai bawa shugaban kasa shawara kan tsaro, Manjo Janar Babagana Munguno mai ritaya ne ya sanar da hakan ga manema labaran fadar shugaban kasa a karshen taro kan tsaro wanda shugaban kasa ya jagoranta.

Babagana Munguno yace Shugaba Buhari ya bada umarnin ne duba da tabarbarewar rashin tsaro da jihar ta Anambra wanda kungiyar ‘yan awaren Biafra ta IPOB suka haifar.

Mai bada shawara akan tsaro yace a watanni biyu da suka gabata sojoji sun samu gagarumar nasara a yakin da suke da ta‘addanci a gabas maso arewacin kasarnan.

Ministan harkokin yan sanda, Maigari Dingyadi wanda shima ya halarci taron ya bayyan jajircewar ‘yan sanda wajen tabbatar da tsaro a jiahar ta Anambra da sauran sassan kasarnan.

Leave a Reply

%d bloggers like this: