Labarai

Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa a jihar Jigawa ta karbi sabbin katinan zabe domin rabawa sabbin wadanda suka yi rijistar a jihar

Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa a jihar Jigawa ta karbi katinan zabe na dindindin dubu 33 da 183 a kashin farko dana biyu na bara domin rabawa sabbin wadanda suka yi rijistar katin zabe a jiharnan.

A sanarwar da mukaddashin sakataren gudanarwa na hukumar, Ibrahim Idris ya bayar, ta shawarci wadanda suka yi rijista da kuma wadanda suka sabinta katinan zaben su a kashin farko da na biyu na bara da su hanzarta zuwa karbar katunan zabensu.

Ya sanar da cewa za a karbi katunan zaben a ofisoshin hukumar na kananan hukumomi a ranakun litinin zuwa juma’a na kowanne mako.

Sanarwar ta bukaci wadanda suka yi rijistar dasu tabbatar sun gabatar da takardar shaidar rijista da aka basu tun da farko kafin karbar katinan zaben nasu na dindindin.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: