

- Gwamna Zulum ya raba wa likitoci fiye da 80 didaje da kudi Naira miliyan 79 don inganta rayuwarsu - July 2, 2022
- Manyan Sarakunan kasar Yarabawa sunyi kiran samun zaman lafiya daga gwamnati kafin zaben 2023 - July 2, 2022
- Kasar Jamus za ta fara dawo wa da Najeriya dubban kayayyakin tarihin ta da aka wawushe tun lokacin mulkin mallaka - July 2, 2022
Kungiyar Miyetti Allah Kautal Hore ta kasa reshen jihar Jigawa ta kaddamar da shirin bunkasa tattalin arzikin Fulani karo na hudu.
A jawabinsa wajen bikin da aka gudanar a cibiyar koyar da sana’o’i ta Limawa dake Dutse, shugaban kungiyar Miyetti Allah ta jiha, Kabiru Umar Dubantu, yace gwamna Badaru Abubakar ne ya yi alkawarin shigar da Fulani cikin shirin bunkasa tattalin arzikin alummar jiharnan.
Kabiru Dubantu yace wannan gwamnati tana shigo da Fulani cikin tsare tsaren ta kamar kowacce alumma.
Ya kara da cewar an ware kudi naira miliyan 40 domin sayo shanu 500 da kuma awaki da za a rabawa Fulani a matsayin bashi da zasu biya a tsawon shekaru biyu zuwa uku.
Yace gwamnatin jihar Jigawa tana kan gaba wajen kula da jin dadin Fulani ta hanyar shigo dasu cikin tsare tsaren gwamnati.
Shugaban na kautal hore yace za a cigaba da rabon shanun da kuma awaki a sassan jiharnan a matsayin rance marar kudin ruwa.