Hukumomi a Burkina Faso sun tabbatar da kisan mutane 80 a harin da aka kai arewacin kasar

0 83

Hukumomi a Burkina Faso sun tabbatar da kisan mutane 80 a harin ranar Laraba da aka kai arewacin kasar.

Wadanda aka kashen sun hada da fararen hula da kuma sojojin gwamnati.

To amma sanarwar ma’aikatar sadarwa ta ce an kashe ‘yan bindiga 80 a kusa da birnin Arbinda.

Harin shine mafi muni a yan kwanakin nan a yankin na Sahel gefen Burkina Faso, da ke da iyaka da kasashen Nijer da Mali da ya zama wata matattarar masu ikirarin jihadi.

Dubban fararen hula sun rasa rayukansu yayin da miliyoyi suka rasa muhallansu daga shekarar 2018 zuwa yanzu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: