Hukumomin EFCC da ICPC sun ce sun samu rauni da rashin kwarin gwuiwa sakamakon afuwar da shugaba Buhari ya yiwa tsohon gwamnan jihar Taraba da na Filato

0 52

Jami’an hukumomin yaki da cin hanci da rashawa a Najeriya EFCC da ICPC, sun ce sun samu rauni da rashin kwarin gwaiwa sakamakon afuwar da shugaban kasa muhammadu Buhari yayiwa  tsohon gwamnan jihar Taraba Jolly Nyame da tsohon gwamnan jihar Filato Joshua Dariye bayan ankama su da laifin cin hanci da rashawa.

Kafin haka dai an yanke wa mutanen biyun hukuncin dauri ne, bayan samun su da laifin satar kudaden jihohinsu.

Jami’an cibiyoyin biyu, a hirarsu da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya NAN, sun koka akan  afuwar da aka yi musu, inda suka zargi shugaban kasa Muhammadu Buhari da yin zagon kasa a yaki da cin hanci da rashawa.

Jami’an sun nemi a sakaya sunansu saboda dalilai na tsaro.

Mista Dariye mai shekaru 64 da Mista Nyame mai shekaru 66, an same su da laifin karkatar da dukiyar jama’a a lokacin da suke gwamnonin jihohinsu.

Amma a ranar Alhamis, a taron majalisar kasar da aka gudanar a fadar shugaban kasa dake Babban birnin tarayya Abuja.

Shugaba Buhari ya yi afuwa ga tsoffin gwamnonin biyu, da kuma wasu 157, bisa dalilai na rashin lafiya da kuma girman shekaru.

Leave a Reply

%d bloggers like this: