Hukumomin lafiya sun tabbatar da barkewar cutar sankarau a kananan hakumomin jihar Jigawa 6

0 274

Hukumomin lafiya sun tabbatar da barkewar cutar sankarau a kananan hakumomin jihar jigawa 6.

Daraktan hakumar lafiya matakin farko na jihar Dr. Shehu Sambo ya bayyana haka yayin kaddamar da gangamin shirin polio a fadar mai martaba sarkjin Dutse Alhaji Muhammad Hamim Nuhu.

A cewarsa an samu barkewar cutar ne a wasu kananan hakumomi dake makobtaka kai tsaye da jamhuriyar Niger.

Kananan hakumomin sun hada da Babura, Birniwa, Malam Madori, Maigatari, Kaugama and karamar hakumar Suletankarkar.

Sambo ya bayyana cewa an kebe wadanda suka harbu da cutar tare da tura tawagar jami’an lafiya yankin domin soma rigakafin cutar a yankunan da abin ya shafa.

Ya kuma shawarci alumma da su dauki matakan kare kai, yayin bacci ta hanyar kwanciya a dakunan dake da wadatacciyar iska da kuma kauracewa cunkoso yayin bacci.

Leave a Reply

%d bloggers like this: