Hukumomin Majalisar Dinkin Duniya na gargadin cewa miliyoyin mutane a Somalia na iya fuskantar yunwa.

Hukumomin sun ce a halin yanzu yara miliyan 1 da dubu 400 na fuskantar matsalar rashin abinci mai gina jiki.

A halin yanzu Somaliya na fuskantar abin da masana suka kira mummunan fari cikin shekaru goma, inda kogin Juba mafi girma a kasar ya kusa kafewa.

A wani labarin kuma, wasu da ake kyautata zaton ‘yan bindiga ne sun kashe sojoji biyar a kasar Benin a wani wajen shakatawa da ke arewacin kasar.

Arewacin Benin ya samu karuwar ayyukan ‘yan tayar da kayar baya saboda kusancinsa da yankunan da ake fama da rikici a makwabtan Burkina Faso da Nijar da Najeriya.

A cikin 2019, an kashe wani jagoran gida tare dayin garkuwa da wasu Faransawa biyu. Daga baya aka sake su.

Haka kuma an kai hare-hare akalla uku kan sojoji a yankin arewacin kasar tun daga watan Nuwamban bara.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: