Labarai

Hukumomin MDD sun ce Najeriya tana bukatar Naira biliyan 147 domin dakile matsalolin tsaro da abinci mai gina jiki da suke addabar yankin Arewa Maso Gabas

Hukumomin Majalisar Dinkin Duniya sun ce Najeriya tana bukatar Naira Biliyan 147 domin dakile matsalolin tsaro da abinci mai gina Jiki da suke addabar yankin Arewa Maso Gabas.

Hukumomin sun hada da Ofishin Hukumar Jinkai, da Shirin Samar da Abinci na Majalisar Dinkin Duniya, da Hukumar Noma na Majalisar Dinkin Duniya da kuma Asusun Tallafawa Kananan Yara na Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF) da sauran su.

Da yake Jawabi a taron Wadata Jiki da Abinci mai gina Jiki a yankin Arewa Maso Gabas, wanda aka gudanar a Abuja, wakilin Hukumar Samar da Abinci a Najeriya Mista Fred Kafeero, ya ce akwai bukatar ayi wani yunkuri mai Nagarta domin kawo dauki a fannin.

Mista Kafeero, ya ce kimanin mutane Miliyan 3 da dubu 400 ne suke bukatar tallafin gaggawa a Jihohin Adamawa, Borno da kuma Yobe.

Haka kuma ya ce hukumomin suna bukatar Dala Biliyan 1 da Miliyan 100 domin kayan agaji ga mutanen da suke Jihohin 3.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: