Ina Shawartar Zababbun Gwamnoni Da Su Saka Hannun Jari Wajen Bunkasa Rayuwar Matasa

0 56

Mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ya shawarci zababbun gwamnoni da su saka hannun jari wajen bunkasa rayuwar matasa domin samun ci gaban tattalin arziki na zamani nan da shekaru kadan masu zuwa.

Yemi Osinbajo ya bayyana haka ne a wajen taron kaddamar da zababbun gwamnonin masu jiran gado wanda kungiyar gwamnonin Najeriya ta shirya jiya a Abuja.

Mataimakin shugaban kasar ya samu wakilcin sakataren gwamnatin tarayya Boss Mustapha.

Yemi Osinbajo ya ce ya zama wajibi a fito da hanyoyin da matasa ke da su, wanda kusan sune kashi 75 cikin 100 na al’ummar kasarnan, ta hanyar amfani da fasahar zamani.

Ya ce matasan kasarnan na bukatar tallafin da zai sanya su zamo masu samar da sana’o’in bunkasa arziki.

Leave a Reply

%d bloggers like this: