Antony Blinken Ya Yi Alkawarin Jajircewar Amurka Wajen Cigaban Dimokuradiyyar Najeriya

0 71

Sakataren harkokin wajen Amurka, Antony Blinken, ya kira zababben shugaban kasa mai jiran gado, Bola Ahmed Tinubu, ta wayar tarho, inda ya yi alkawarin jajircewar kasarsa wajen cigaban dimokuradiyyar Najeriya.

Kakakin gwamnatin Amurka Mathew Miller ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar jiya.

A cewar kakakin zababben shugaban kasar Tunde Rahman, jami’in diflomasiyyar na Amurka ne ya fara kiran wayar. Tunde Rahman ya nakalto Anthony Blinken na shaidawa zababben shugaban kasar cewa idan babu hadin kan kasa, da tsaro, da ci gaban tattalin arziki da shugabanci na gari, Najeriya ba za ta zama kasa mai kyau ba, kuma baza ta iya taka rawar da ta dace ba tsakanin kasashen Afirka.

Leave a Reply

%d bloggers like this: