‘Yan Arewa Ne Suka Jawo Halin Da Ake Ciki Na Koma Bayan Ilimi A Arewa

0 71

Ministan Ilimi Malam Adamu Adamu a jiya ya ce ‘yan Arewa ne suka jawo halin da ake ciki na koma bayan ilimi a Arewa.

Ya yi jawabi ne a Abuja a wajen taron baje kolin manhaja koyarwa a jami’o’i da kuma wani littafin da aka rubuta domin karrama shi.

Adamu Adamu ya ce yayin da mata musulmi ne suka kafa jami’o’i biyu na farko a duniya, a nan Arewa kuma ana amfani da addinin Musulunci wajen hana mata fita daga gida.

Adamu Adamu ya yabawa hukumar kula da jami’o’i ta kasa bisa yunkurinta na ganin an samu karuwar jami’o’i masu zaman kansu a kasarnan.

Ya ce kokarin hukumar yana samun sakamako mai kyau tare da kara samar da jami’o’i a arewacin Najeriya a ‘yan kwanakin nan. Ya bayyana jin dadinsa da cewa a cikin sabbin jami’o’i masu zaman kansu 37 da majalisar zartarwa ta tarayya ta amince da su a wannan makon, mafiya yawansu a Arewa suke.

Leave a Reply

%d bloggers like this: