Yajin Aikin Da Likitoci Masu Neman Kwarewa Suka Fara Ya Saba Wa Doka

0 55

A jiya ne gwamnatin tarayya ta bayyana yajin aikin gargadi na kwanaki biyar wanda likitoci masu neman kwarewa suka fara a yau da cewa ya sabawa doka.

Ta ce kungiyar likitoci masu neman kwarewa ta kasa ba ta ba da gargadi na kwanaki 21 kafin fara yajin aikin ba, kamar yadda dokar aiki ta tanada.

Kakakin ma’aikatar kwadago da samar da ayyukan yi, Olajide Oshundun, a wata zantawa da ya yi da manema labarai, ya ce ministan ya karbi wasikar kungiyar masu neman kwarewa a jiya.

Ya ce wasikar, mai dauke da kwanan wata 15 ga Mayun da muke ciki, yakamata a aiko ta da wuri domin cika sharudan bayar da gargadi na kwanaki 21. A ranar 29 ga Afrilu ne kungiyar likitoci masu neman kwarewa ta ba da wa’adin makonni biyu ga gwamnati, ta aiwatar da yarjejeniyoyin da aka cimma ko kuma ta fuskanci yajin aiki.

Leave a Reply

%d bloggers like this: