NDLEA Ta Kama Wasu Mutane 85 Da Ake Zargi Da Safarar Kwayoyi A Wani Gidan Rawa Da Ke Kano

0 63

Hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA, ta kama wasu mutane 85 da ake zargi da safarar kwayoyi a wani gidan rawa na dare da ke Kano.

A wata sanarwa da ya fitar jiya a Kano, kwamandan hukumar na NDLEA a jihar, Abubakar Idris-Ahmad, ya ce kamen ya biyo bayan korafe-korafe da ake yi kan ayyukan da suka shafi muggan kwayoyi a gidan rawar.

Ya ce makotan gidan rawar sun koka kan yadda aka mayar da gidan rawar wurin shan miyagun kwayoyi.

Ya kara da cewa wadanda aka kama sun hada da maza 55 da mata 30 kuma an samu wasu abubuwa a wajensu da ake kyautata zaton tabar wiwi ce.

Idris-Ahmad ya kuma ce wasu daga cikin wadanda ake zargin sun yi yunkurin tsira daga kamen ta hanyar tsallaka Katanga yayin da wasu kuma suka yi kokarin buya a cikin firiza amma duk da hakan an kama su. Ya ce wadanda ake zargin na fuskantar bincike domin tantance masu sayar da kwayoyi a cikinsu kafin a gurfanar da su a gaban kuliya.

Leave a Reply

%d bloggers like this: