Shugaba Buhari Ya Dawo Abuja Bayan An Duba Lafiyar Hakorinsa A Landan

0 91

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya dawo Abuja bayan ya bi sahun sauran shugabannin kasashen duniya domin halartar bikin nadin sarautar Sarki Charles na Uku a matsayin Sarkin Birtaniya kuma shugaban kungiyar Commonwealth.

Kamfanin Dillancin Labarai na kasa ya bayar da rahoton cewa, shugaban kasar wanda ya sauka a Abuja da yammacin jiya, ya tsawaita zamansa a Landan bayan nadin sarautar da karin mako guda domin neman lafiya.

Mai magana da yawun shugaban kasar, Femi Adesina, a wata sanarwa da ya fitar a ranar 10 ga watan Mayu ya ce, shugaban kasar zai cigaba da kasancewa a birnin Landan na tsawon mako guda, bisa umarnin likitan hakori, wanda ya fara zuwa wurinsa.

Yayin da yake birnin Landan, shugaba Buhari ya halarci taron kasashen kungiyar Commonwealth inda ya sake bayyana gamsuwarsa da yadda zaben 2023 ya gudana a Najeriya. Shugaban kasar ya kafa hujja ne da yawan fitowar masu kada kuri’a da kuma yanayin zaman lafiya da aka samu yayin gudanar da zaben.

Leave a Reply

%d bloggers like this: