INEC ta bayyana zaben gwamnan jihar Anambra a matsayin wanda bai kammalu ba

0 95

Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa wato INEC ta bayyana zaben gwamnan jihar Anambra a matsayin wanda bai kammalu ba.

Farfesa Florence Obi, baturiyar zaben jihar, ta sanar da hakan ne a ofishin hukumar INEC da ke Awka, babban birnin jihar Anambra a sa’o’in farko na ranar Litinin.

Ta ce ba za a iya bayyana wanda yayi nasarar zaben ba saboda ba a yi zabe ba a karamar hukumar Ihiala ta jihar.

A yayin kare abinda suka aikata a dokar zabe, Obi ta ce za a yi zaben maye gurbi a karamar hukumar Ihiala a ranar Talata.

Leave a Reply

%d bloggers like this: