Mataimakin Shugaban Jami’ar Abuja, Farfesa Abdul-Rasheed Na-Allah, yace hukumar makarantar ta dauki tsattsauran mataki akan malaman da ke lalata da dalibai.

Ya kara da cewa tini suka kori farfesoshi biyu saboda laifin.

Na’Allah ya shaidawa Kamfanin Dillancin Labarai na kasa NAN a yau a birnin New York cewa.

Jami’ar bata da wata manufa ta cin zarafin mata a harabar jami’ar.

Na-Allah, wanda ya kai ziyarar kwana biyu a kasar Amurka domin ganawa da kungiyar tsofaffin daliban Jami’ar, reshen Amurka, domin neman tallafi ga makarantar.

A cewarsa, jami’ar ta himmatu wajen bin kyawawan dabi’u kuma ba za ta amince da duk wani aiki na rashin da’a ba.

Jami’ar tana aiki ba dare ba rana domin ganin karatu da tarbiya a fadin kasar nan.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: