Jam’iyar APC ta fitar da jadawalin ranakun gudanar da zabukan shugabannin ta na Jihohi

0 96

Jam’iyar APC mai Mulki, ta fitar da Jadawalin ranakun gudanar da zabukan Shugabannin ta na Jihohi wanda za’a gudanar a ranar 16 ga watan Octoba.

Sakataren Jam’iyar na rikon Kwarya, Sanata John James Akpanudoedehe, shine ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da aka rabawa manema labarai a Abuja.

Sanarwar ta ce an fara sayar da Form din masu sha’awar tsayawa Takarar shugabancin Jam’iyar na Jihohi tun daga ranar 15 ga watan Satumba, kuma za’a kallama a ranar 11 ga watan Octobar da muke ciki.

Za’a kuma a tantance yan takarkaru a ranakun 13 da 14 ga watan Octoba na shekarar 2021, da muke ciki, inda kuma za’a gudanar da zaben a ranakun 16 ga watan Octoba a dukkan Jihohin da suke Najeriya, in banda Jihohin Anambra da Zamfara.

Haka kuma, za’a fara sauraren korafe-korafen yan neman takarar wanda basu yi nasara ba, a ranakun 23 zuwa 30 ga watan Octoba na wannan shekara.

Sakataren Jam’iyar ya ce Masu neman takarar shugaban Jam’iyar na Jihohi zasu sayi Forms akan Naira dubu 100,000, inda kuma masu neman Mataimakin Shugaban Jam’iyar na Jiha, da sakataren Jam’iya da Ma’aji zasu sayi Form din akan Naira dubu 50,000.

Leave a Reply

%d bloggers like this: