Wadanda aka zaba sun hadar da Dr Babandi Ibrahim Gumel a matsayin shugaba da Umar Danjani mataimakin shugaba da Mohammed Bahutu Sakatare da Isyaku Maruta mai baiwa jamiyya shawara kan Harkokin Shari’a da Umar Kyari Jitau Sakataren Yada Labarai da Kabiru Nura sakataren Tsare-Tsare da Hajia Murja Garki shugabar Mata da kuma Ali Badala OditaJam’iyyar PDP reshen Jihar Jigawa ta zabi sabbin shugabanni.Jam’iyyar PDP reshen Jihar Jigawa ta zabi sabbin shugabanni
.
Shugaban kwamitin shirya babban taron jamiyyar , Isa Ahmed, ya ce daga cikin wakilai 888 da aka tantance, 875 ne suka kada kuri’unsu.
A jawabinsa sabon shugaban jamiyyar PDP na jiha Dr Babandi Ibrahim ya bukaci ‘yan jam’iyyar da su ci gaba da zama tsintsiya madaurinki daya domin ci gaban jam’iyyar.
A nasa jawabin tsohon gwamnan jihar, Alhaji Sule Lamido, ya shawarci sabbin shugabannin da su hada kan jam’iyyar tare da jagoranci cikin hikima da karfin siyasa domin ceto al’ummar jihar da sauran ‘yan Najeriya daga halin kunci da ake ciki.