Jam’iyyar PDP Ta Kawo Shaidu Uku A Wani Bangare Na Karar Da Ta Shigar Na Kalubalantar Sakamakon Zaben Shugaban Kasa

0 442

Shaidun dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, sun shaida wa kotun sauraron kararrakin zaben shugaban kasa cewa alkalan zaben ba su mika sakamakon zaben shugaban kasa da aka gudanar a ranar 25 ga watan Fabrairu kai tsaye daga rumfunan zabe ba.

A jiya ne jam’iyyar PDP ta kawo shaidu uku a wani bangare na karar da ta shigar na kalubalantar sakamakon zaben shugaban kasa.

Shaidu sun hada da jami’an tattara bayanai na jihohi kamar Mohammed Sani Idris Kutigi (Niger), Nicholas Msheliza (Borno) da Silas Joseph Onu (Ebonyi).

Da take ba da shaida a amsa tambayoyin da lauyan hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC), Kemi Pinheiro, babbar lauyan Najeriya (SAN), Msheliza ,ta ce saboda gaza fitar da sakamakon zabe na rumfunan zabe dubu 5 da 71 a jihar, ta kara da cewa sakamakon ya sha banban da wanda wakilan jam’iyyar suka gabatar masa a matakai daban-daban.

Shima da yake ba da shaida, Kutigi ya ce ba a shigar da sakamakon zabe daga rumfunan zabe dubu 4 da 948 na jihar zuwa tashar zabe ta INEC ba.

Leave A Reply

Your email address will not be published.