Hukumar Kula da Man Fetur ta Najeriya, NMDPRA, ta ce ba za ta sake kayyade farashin man fetur ba.
Shugaban Hukumar, ACE, Farouk Ahmed, wanda ya bayyana haka a wani taron manema labarai a Abuja jiya Juma’a, ya ce daga yanzu yan kasuwa ne za su kayyade farashin a karkashin kasuwar mai sassaucin ra’ayi.
Wannan dai ya biyo bayan cire tallafin da gwamnatin tarayya tayi.
Shugaba Bola Tinubu a jawabinsa na farko a ranar Litinin ya ce tsarin tallafin man fetur ya kare da fara gwamnatinsa.
Tinubu, ya ce a yanzu kasuwar ta bude ga duk wanda zai shigo da shi idan ya cika dukkan bukatu. A cewar Tinubu, aikin NNPC shine ta gyara farashin man fetur din da ta shigo da shi daga kasashen waje da kuma rashin karbar ragamar hukumar.