Jam’iyyun APC Da PDP Sun Samu Rashin Jituwa A Kan Sakamakon Zaben Shugaban Kasa Na 2023

0 79

Jam’iyya mai mulki ta, APC, da babbar jam’iyyar adawa ta PDP, a jiya, sun samu rashin jituwa a kan sakamakon zaben shugaban kasa na 2023.

Yayin da jam’iyyar PDP ta bayyana nasarar zababben shugaban kasa, Asiwaju Bola Tinubu na APC a matsayin dan takarar zabe da bai kamata a bar shi ya tsaya ba, jam’iyyar APC ta yi tir da cewa nasarar da dan takararta na shugaban kasa ya samu ya nuna muradin ‘yan Najeriya.

Jam’iyyar mai mulki ta kara da cewa ba ta samar da na’urorin tantance masu kada kuri’a na BVAS, da aka yi amfani da su wajen gudanar da zaben da hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa, INEC, kamar yadda PDP ta yi zargin.

Kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar PDP, PCC, ta ce idan har Najeriya ta dawo da martabarta a cikin kungiyoyin kasa da kasa, ba za a bar sakamakon zaben shugaban kasa na 2023 da INEC ta sanar ba.

Daraktan tsare-tsare da dabaru na jam’iyyar PDP PCC, Don Pedro Obaseki ne ya bayyana hakan a wata tattaunawa da manema labarai a Abuja, jiya.

Leave a Reply

%d bloggers like this: