NCDC Ta Sami Rahohoton Bullar Zazzabin Lassa Guda 846 A Cikin Jihohi 25

0 122

Cibiyar Kula da Cututtuka ta Najeriya ta sami rahoton bullar cutar zazzabin Lassa guda 846 a fadin kananan hukumomi 99 a cikin jihohi 25.

Mafi girman rukunin shekarun da abin ya shafa shine shekaru 21-30.

Yawanci mutane kan kamu da cutar ta Lassa ta hanyar kamuwa da abinci ko kayan gida da suka gurbace da fitsari ko najasar berayen Mastomy da suka kamu da cutar.

Cutar dai ta yadu ne a yawan berayen da ke sassan yammacin Afirka.

Zazzabin Lassa na ci gaba da zama babban kalubale ga lafiyar al’umma saboda rashin tsaftar muhalli, rashin sanin ya kamata, da kuma bayyanar cututtuka a makare na kara ruruta wutar annobar a Najeriya.

Leave a Reply

%d bloggers like this: