Jam’iyyar ta shigar da kara a gaban kotun sauraron kararrakin zaben gwamna ta nemi a sake zaben gwamnan jihar Borno.
Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta bayyana gwamnan jihar mai ci, Babagana Umara Zulum a matsayin wanda ya lashe zaben ranar 18 ga watan Maris.
Sai dai a yayin da take kalubalantar sakamakon zaben, jam’iyyar NNPP a cikin wata kara da ta shigar ta yi ikirarin cewa hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta cire sunan dan takararta Umar Alkali da tambarin jam’iyyar a cikin takardun zabe.
Sakataren kotun, Mista Taiwo Adediji, ya ce kotun ta karbi kararraki 10 na zaben ‘yan majalisar dokokin kasar.
Ya ce wadannan sun hada da koke-koke guda uku na neman kujerar Sanata da bakwai na majalisar wakilai.
Ya tabbatar da koke guda biyu daga ‘yan takarar jam’iyyar PDP a mazabar Askira/Uba da Kala-Balge na kalubalantar nasarar da ‘yan takarar APC suka samu a yankin.