Kamfanin NNPC ya ce bai umarci yan Kasuwar Man su kara farashin fetur ba akan wanda gwamnati ta kayyade

0 97

Kamfanin Man Fetur na Kasa NNPC, ya ce bai umarci yan Kasuwar Man su kara farashin fetur ba akan wanda gwamnati ta kayyade.

Kungiyoyin yan Kasuwar Man Fetur din sun bayyana cewa sun kara farashin ne fiye da na Gwamnati, saboda kudaden da ake kashewa wajen safarar sa.

Gwamnatin tarayya ta ce har yanzu farashin yana nan akan Naira 165 akan Lita daya, sai dai Dillalan Man fetur din sun ki amincewa da tsarin.

Da yake zantawa da manema labarai ta wayar Tarho, Shugaban Sashen Hulda da Jama’a na Kamfanin Malam Garba Deen Muhammad, ya ce hukumar bata bawa yan Kasuwar umarnin kara karashin ba.

An tuntubi, Kakakin Hukumar Kula da Harkokin Sarrafa Man Fetur da Tacewa da Sufuri ta Kasa Mista Apollo Kimchi, sai dai bai amsa wayar ba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: