Shugaban Kungiyar ASUU ya ce wa’adin mako biyu da shugaban kasar ya bayar domin kawo karshen yajin aikin ya yi yawa

0 76

Shugaban Kungiyar Malaman Jami’o’i ta Najeriya ASUU ya ce wa’adin mako biyu da shugaban kasar ya bayar domin kawo karshen yajin aikin ya yi yawa.

A wata hira da gidan talabijin na Channels Tv, shugaban na ASUU Farfesa Emmanuel Osodeke ya ce a bangarensu na malaman jami’a, cikin kwanaki biyu za a iya warware wannan matsala.

A cewarsa, mako biyu ya yi yawa, za’a iya kammala tattaunawa domin cimma matsaya, hakan kuma ba zai wuce kwana biyu ba

Farfesa Emmanuel Osodeke ya ce a kowacce shekara ‘yan Najeriya na kashe kusan biliyan 200 wajen biyan kudin makaranta a jami’o’in kasar Ghana.

Shugaban ya ce ya kamata gwamnati ta bai wa bangare ilimi fifiko a kasar nan, saboda dukkan yan Najeriya sun je makaranta.

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari a jiya ya umarci Ministan Ilimi na Kasa Malam Adamu Adamu, ya kawo karshen yajin aikin da Jami’oi suke yi cikin Makonni biyu.

Tun a ranar Litinin 14 ga watan Fabrairu ne kungiyar ASUU, ta tsunduma yajin aikin gargadi ga gwamanatin Najeriya na tsawon wata guda sai dai daga baya ƙungiyar ta mayar da yajin aikin na Illa Masha Allahu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: